Bayanin Likita Game Da Alakar Rigar Nono Da Ciwon Nono Wato Breast Cancer

 Ciwon nono, wanda ake kira da (Mastalgia) a Turance na daga cikin matsalolin da mata da dama ke fuskanta a rayuwarsu. Wannan ciwo yana iya kasancewa mai sauƙi ko mai tsanani, wasu lokutan kuma yana da alaƙa da sauyin hormone ko wasu cututtuka.

Ciwon Nono

Ciwon nono na iya kasancewa sakamakon sauyin hormone, infection, ko wani yanayi mai sauƙi. Amma idan ciwon ya tsananta ko kuma aka lura da sauyin siffa ko zubar ruwa daga nono, dole a nemi taimakon likita.

Shin Sanya Matsattsiyar Rigar Nono Na Haddasa Ciwon Kansa?

"Haka nan ba gaskiya ba ne cewa sanya matsattsiyar rigar mama zai haifar da kansar nono. Idan mace ta sa matsattsar rigar mama, hakan na yin illa ga jiki. Saboda zufa za ta iya sa fata ta goge.

"Sanya matsattsiyar rigar mama zai sa a riƙa jin zafi a wuraren da rigar ta ɗame jiki. Saboda haka ya kamata mata su zaɓi rigar mama mai girma daidai-wa-daida. Kuma kada su yi fargabar cewa za ta haifar musu da ciwon kansa," in ji likitar.

"Fitar ruwan nono haka kawai abu ne da yakan faru da mata masu girman nono. Kuma za su iya samun ciwon baya. Saboda haka sanya rigar mama za ta taimaka wajen alkinta nonon.

"Hakan zai iya kare kamuwa da ciwon baya. To amma mu sani cewa ita rigar mama tana taimakawa ne na wani dan lokaci. Idan kika ji kina jin zafi a lokacin da kika sa rigar mama, to ki daina sawa."

"Saboda haka rigar mama ba ta da wani tasiri kan ingancin nono. Babu amfani kuma babu cutarwa," in ji dakta Balkumari.

Post a Comment

Previous Post Next Post