Wani bincike daga Jami’ar North Carolina State University (NC State) ya gano cewa yawaitar kyankyasai(cockroach) a cikin gida na iya jawo asma, tari da matsalolin numfashi, saboda suna fitar da ƙwayoyin guba da ƙura masu haddasa rashin lafiya.
Masu binciken sun bayyana cewa gidajen da ke da ƙwari da yawa suna ɗauke da adadi mai yawa na endotoxins wani sinadari da ke fitowa daga ƙwayoyin cuta da suka mutu.An gano cewa kyankyasai mata suna samar da ninki biyu na wadannan gubobi fiye da maza, musamman a ɗakunan girki da ke da abinci.
Binciken ya kuma nuna cewa yin amfani da maganin kashe ƙwari cikin tsari yana rage waɗannan ƙwayoyin guba da ƙura masu haddasa rashin lafiya.
Masana sun jaddada cewa tsabtace gida da kawar da ƙwari na da matuƙar muhimmanci domin kare lafiyar jama’a da inganta iskar cikin gida.