Kamar yadda aka bayyan a shafin Datti Asalafy na Fezbuk, wasu bayanai daga sansanin ƙungiyoyi na ta'addanci a yankin Arewa na nuni da cewa hankalin Shugabannin ƙungiyoyi na ta'addanci ya yi mummunan tashi bayan sun samu labarin gargaɗin da Amerika ta yi na cewa za ta ƙaddamar musu da hari.
An ce a halin da ake ciki yanzu, manyan Shugabanni na ta'addanci suna ta guduwa daga sansaninsu zuwa kan iyakokin ƙasarmu Nigeria domin su kauce wa harin Amurka
Manyan 'yan ta'adda da suke da horo a kan ta'addanci sun fi kowa sanin cewa Amerika za ta riske su a duk inda suka ɓuya cikin Nigeria, saboda sun san tana da kayan aikin tsaro na fasahar zamani da take ganin motsinsu, don haka suna da masaniyar cewa Amerika tana ganinsu, tana ganin har ɗakin da suke kwana
Sannan manyan Shugabannin ta'addancin suna ganin abinda Amerika take yi wajen aika makamai masu linzami da suke isa kowani kusurwa na duniya irin su Intercontinental Ballistic Missiles su kashe duk wanda suke son kashewa
Wadannan dalilai ya sa a halin da ake ciki yanzu duk wanda ya bunƙasa a jagorancin ta'addanci ya gudu daga sansaninsa, wasu manyan 'yan ta'addan har sun fice daga cikin Nigeria
Sannan ku lura a cikin kwana biyun nan jami'an tsaro suna ragargazar 'yan ta'adda tare da kuɓutar da waɗanda aka yi garkuwa da su, domin sansanin ta'addancin ya rikice, kowa yana guduwa, suna neman inda za su ɓoye. Allah Ka kare mana Kasarmu Nigeria, Ka mana maganin 'yan ta'adda da waɗanda suke taimakonsu ta kowace irin hanya.
