Dubban ɗaruruwan ‘yan ƙasa a Amurka sun fito kan tituna suna zanga-zangar neman a sauke Shugaba Donald Trump daga mulki, sakamakon yadda suka ce ya gaza jagorantar ƙasar cikin adalci da gaskiya.
Masu zanga-zangar sun taru a gaban Fadar Gwamnatin White House, inda suka rera wakoki da ɗauke da kwalaye masu ɗauke da rubuce-rubuce kamar “Justice for All” da “Trump Must Go.”
Wasu daga cikin masu zanga-zangar sun bayyana cewa suna ganin Trump ya kawo ƙarin rarrabuwar kai a cikin al’umma, yayin da wasu ke zargin sa da matsanancin amfani da iko da kuma tsoratar da ‘yan adawa.
Rundunar ‘yan sanda ta Washington DC ta tabbatar da cewa ta ɗauki matakan tsaro na musamman don guje wa tashin hankali, yayin da ake cigaba da gudanar da taron cikin lumana.
Sai dai fadar gwamnatin Trump ta ce zanga-zangar ba ta da wani tasiri ga mulkinsa, tana mai cewa Shugaban zai ci gaba da mayar da hankali kan ci gaban tattalin arzikin Amurka da kare martabar ƙasar a duniya.
Masana siyasa na ganin cewa wannan zanga-zanga na iya ƙara matsin lamba kan gwamnatin Trump, musamman idan ta ci gaba da yawaita a manyan biranen ƙasar.