An bayyana cewa mutum mafi arziƙi a duniya yanzu yana da damar da ba a taɓa samu ba, wato damar zama trillionaire na farko a tarihin bil’adama.
Masana harkar kuɗi sun bayyana cewa dukiyarsa tana ƙaruwa ne saboda haɓakar kamfanoninsa a kasuwar hannayen jari da kuma zuba jari mai yawa a fannin fasaha da sararin samaniya.
Rahotanni sun nuna cewa idan wannan yanayin tattalin arziƙi ya ci gaba da gudana kamar yadda yake, darajar dukiyarsa na iya haura dala tiriliyan ɗaya cikin ‘yan shekaru masu zuwa, abin da ba a taɓa gani ba a tarihin duniya.
Wasu suna ganin wannan abin koyi ne, jajircewa da ƙirƙira, amma wasu kuma suna ganin hakan yana nuna irin yadda giɓin arziƙi ke ƙaruwa tsakanin masu kuɗi da talakawa.
Masana tattalin arziki sun kuma nuna damuwa cewa irin wannan tarin dukiya a hannun mutum ɗaya na iya tasiri ga siyasa da adalcin tattalin arzikin duniya.