Mazauna Unguwar Fagge A Jihar Kano Sun Shigar Da Korafi Saboda Karin Naira 570,00 A Kan Kudin Hayar Shaguna

Mazauna layin Sabo Ringim da kewaye a mazaɓar Fagge a ƙaramar hukumar Fagge a jihar Kano, sun shigar da ƙorafi a rubuce ga shugaban ƙaramar hukumar akan wani ƙarin kuɗin hayar shaguna da aka yi musu.

Shaguna A Kano

Mazauna unguwar, ƙarƙashin kungiyar cigaban al'umma mai suna Restore Fagge Community, sun yi zargin wani attajiri, Alhaji Balarabe da tsuga musu kuɗin hayar shaguna daga Naira dubu 30 zuwa Naira dubu 600, karin Naira dubu 570 kenan a wani gida da ya siya daga magadan marigayi Alhaji Musa Gwadabe.

A takardar korafin, mai ɗauke da kwanan watan 12 ga watan Nuwamba, wacce su ka miƙa ta hannun mataimakin shugaban ƙaramar hukumar, Hon. Nura Ali Shugaba a jiya Laraba, mazauna unguwar sun ce tun asali ma Naira dubu 8 suke biya a shaguna 10 da ke jikin gidan, inda daga bisani saboda yanayin rayuwa, farashin ya karu zuwa Naira dubu 30.

A cewar mazauna unguwar, bayan gida ya zama na magada, sai su ka siyarwa da shi Alhaji Balarabe da ya ke kasuwar Kantin Kwari.

Bayan ya siya, a cewar su, sai ya umarci mazauna shagunan da cikin gidan su tashi zai yi gyara, in ya so idan ya gama zai dawo da su.

To bayan ya kammala gyaran gidan, inji yan ƙungiyar, sai  ya tattauna da  mutanenshi inda su ka bashi shawarar ya maida kuɗin hayar shagunan Naira dubu 600,000 a shekara.

Sun yi zargin cewa duk wanda zai kama shago sai dai ya fara biyan na shekara biyu, wato Naira miliyan daya da dubu dari biyu (N1,200,000).

Sun yi korafin cewa yawancin su teloli ne, sun ce wannan tashin gwauron zabin zai yi wa sana'ar su illa matuƙa, tunda sai azumi ya zo suke samun dinkin da yawa.

A cewar su, idan aka tafi a haka, sauran masu gidaje su ma za su ƙara kuɗin hayar nasu shagunan, inda su ka ce hakan zai ƙara karya sana'ar ta su da dama ta dade ta na tangal-tangal.

A takardar korafin, wacce su ka kuma tura kwafin ta ga hukumomin tsaro, sun roki ƙaramar hukumar da hukumomin da suka dace da su kawo musu dauki.

A jawabin sa bayan karɓar takardar korafin, mataimakin shugaban ƙaramar hukumar ya ci alwashin daukar matakin da ya dace don ganin an warware matsalar.

Ya baiyana cewa karamar hukuma za ta gayyaci Mai gidan ta tattauna da shi domin samun mafita.

Ya kuma yabawa Kungiyar bisa daukar wannan mataki na doka da kuma fafutukar wajen kawo ci gaban al'umma.

Post a Comment

Previous Post Next Post