Babbar jam'iyyar adawa a Najeriya, PDP na ci gaba da nutsewa cikin rikici bayan da kotuna daban-daban ke bayar da mabambantan hukunce-hukunce game da babban taronta na ƙasa.
A ranar Talata wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta sake dakatar da jam'iyyar daga gudanar da babban taronta da take shirin yi a garin Ibadan na jiyar Oyo.Wannan shi ne karo na biyu da kotu ta hana gudanar da taron, wanda babbar jam'iyyar hamayyar ke shirin yi a ranakun 15 zuwa 16 ga watan Nuwamba.
Sai dai kafin wannan hukuncin na biyu, wata kotun a jiyar Oyo ta umarci jam'iyyar da ta ci gaba da gudanar da shirye-shiryenta na babban taron, wanda hakan ya haifar taraddudi.
A wannan shari'a ta baya-baya, tsohon gwamnan jihar Jigawa Sule Lamido ne ya shigar da ƙara yana ƙalubalantar hana shi yin takarar shugabancin jam'iyyar.