Saraki Na Neman PDP Ta Dakatar Da Taronta

Tsohon Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Bukola Saraki ya shawarci jam'iyyarsu ta PDP mai adawa ta dakatar da shirin gudanar da babban taronta na ƙasa a jihar Oyo saboda umarnin kotuna kan hakan.

Saraki ya bayar da shawarar cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na dandalin X ranar Laraba bayan wata ganawa da kwamatin sasanta 'ya'yan jam'iyyar ƙarƙashin jagoracin Hassan Adamu.

Tsohon shugaban da ya jagoranci majalisa daga 2015 zuwa 2019 ya ce umarnin kotuna kusan huɗu masu karo da juna game da babban taron zai iya jawo matsala game da halaccin duk wani mataki da ya biyo bayan taron.

Zuwa yanzu, akwai ƙararraki uku a gaban kotuna daban-daban waɗanda suka bayar da umarnin a dakata da shirin taron da kuma akasin haka, yayin da PDP ta ce tana ci gaba da shirin gudanar da shi a ranakun 15 da 16 ga watan Nuwamban nan.

Ministan Abuja Nyesom Wike, da tsohon Gwamnan Jigawa Sule Lamido na cikin waɗanda suka kai jam'iyyar kotu kan taron.

Post a Comment

Previous Post Next Post