Nijeriya Ba Za Ta Rasa Komai Ba Don Ta Yanke Alaka Da Amurka, In Ji Sheikh Ahmad Gumi

Fitaccen Malamin Addinin Musuluncin nan na Nijeriya Sheikh Ahmad Mahmud Gumi ya bayyana cewa babu abin da Nijeriya za ta ragu da shi idan ta daina hulɗa da Amurka.

Sheikh Ahmad Gumi

Ya bayyana haka ne a cikin ɓangaren wata hira da TRT Afrika Hausa ta yi da shi a daidai lokacin da ake ci gaba da ce-ce-ku-ce kan barazanar da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi wa Nijeriya na ɗaukar matakin soji a kanta.

“Ba Amurka ce kaɗai ƙasa a duniya ba da har za ka rasa wani abu idan ka daina hulɗa da ita, idan kayan ƙere-ƙere ne akwai China, idan kayan ƙarfi ne [makamai] akwai Rasha,” in ji Sheikh Gumi.

“Akwai ƙasashe da suke rayuwa waɗanda ba su san akwai wani abu Amurka ba, wannan ƙasar ba ta nuna mana tana ƙaunarmu ba, sai dai ta tatse manmu, ta raba mu, ta cutar da mu,” kamar yadda ya ƙara da cewa.

Sheikh Gumi ya jaddada cewa Amurka ba ta neman Nijeriya da alkhairi inda ya yi zargin cewa Amurkar na cikin waɗanda suka rinƙa taimaka wa yankin Biafra da ke son ɓallewa daga Nijeriya a lokacin yaƙin basasa.

Fitaccen malamin ya bayyana cewa Musulmai da Kirista suna zaune lafiya, babu ƙamshin gaskiya a kalaman Trump na Musulmi na kashe Kiristoci a Nijeriya.

Post a Comment

Previous Post Next Post