Tinubu Ya Zaftare WA Yan Arewa ₦760,915.83 A Kan Kudin Kowace kujera Ta Zuwa Aikin Hajji Mai Zuwa

Tinubu Ya Zaftare WA Yan Arewa ₦760,915.83 A Kan Kudin Kowace kujera Ta Zuwa Aikin Hajji Mai Zuwa. Hukumar jin daɗin Alhazai ta kasa ta sanar da rangwamen da gwamnatin Tarayya ta yi  wa Musulman Nijeriya, masu niyyar zuwa sauke aikin faralin 2026 a kasar Saudiya

Alhazai

A watan da ya gabata ne dai shugaban kasa Tinubu ya ba hukumar umurnin da ta gaggauta zaftare wa musulman Nijeriya wani abu daga cikin kudaden zuwa aikin Hajjin. 

Kamar yadda hukumar ta sanar, yanzun yan shiyar Arewa maso Gabas da suka hada da yankin Borno/Adamawa za su biya ₦7,579,020.96 sun sami ragowar ₦748,104.63 a kan yadda aka fitar da farashin a baya. 

Sai sauran jihohin Arewacin Najeriya, su kuma za su biya ₦7,696,769.76 a kan kowace kujera, inda su kuma suka sami rarar ₦760,915.83

Wadanda za su tashi a jihohin Kudu kuwa, za su biya ₦7,991,141.76 a kan kowace kujerar aikin hajji, inda suka sami ragowar ₦792,943.83 kenan

Kamar yadda majalisar Katsina Daily News ta rawaito, hukumar ta kuma kara wa'adin ci gaba da biyan kudin zuwa aikin Hajjin har zuwa 5 December 2025

Post a Comment

Previous Post Next Post