Koriya Ta Kudu Ta Gurfanar Da Tsohon Shugaba Yoon Kan Zargin Taimaka Wa Makiyi

 Mahukunta a ƙasar Koriya ta Kudu sun gurfanar da tsohon shugaban ƙasar Yoon Suk Yeol a gaban kotu bisa zargin taimaka wa maƙiya, wanda ke zama ɗaya daga cikin manyan rikice-rikicen siyasa da suka girgiza ƙasar a ‘yan shekarun nan.

tsohon shugaban ƙasa Yoon Suk Yeol

A cewar ofishin mai gabatar da ƙara na babban birnin Seoul, an zargi Yoon da bayar da bayanan sirri na ƙasa ga wata ƙasa ta waje a lokacin da yake mulki, zargi da shi kuma ya musanta ƙwarai. Rahotanni sun bayyana cewa, wannan shari’a na da alaƙa da zargin karya dokokin tsaro da kuma yin hulɗa da jami’an da ke da alaka da ƙasar Koriya ta Arewa ba tare da izini ba.

Lauyoyin Yoon sun bayyana tuhumar a matsayin “shiri na siyasa”, suna cewa abokan hamayyarsa ne ke ƙoƙarin bata masa suna kafin zaɓen da ke tafe.

Wannan tuhuma ce ta farko a cikin shekaru masu yawa da aka taba zargin tsohon shugaban Koriya ta Kudu da irin wannan laifi mai tsanani na tsaron ƙasa. Idan aka same shi da laifi, Yoon na iya fuskantar hukuncin ɗaurin shekaru da dama a gidan yari.

Fadar shugaban ƙasa ta ƙi yin tsokaci kan lamarin, sai dai wannan shari’a ta tayar da muhawara mai zafi a ƙasar, inda magoya bayansa ke kiran ta “farautar siyasa,” yayin da masu suka ke neman a tabbatar da gaskiya da adalci.

Post a Comment

Previous Post Next Post