Gwamnatin Birtaniya ta shawarci yan kasarta su ƙauracewa yin balaguro a wasu sassan Najeriya bayan nuna damuwa kan ƙaruwar hare-haren ta'addanci da satar mutane.
Sanarwar da Gwamnatin Birtaniya ta fitar a shafinta na intanet a ranar Lahadi ta ce matsalar tsaro na ci gaba da ƙaruwa a Najeriya, kuma satar mutane da aikata laifuka da rikicin ƙabilanci sun shafi dukkanin sassan ƙasar.
Wannan na zuwa yayin da Gwamnatin ta ce alkalumman da ta tattara sun nuna ana samun nasarar shawo kan matsalar tsaron da ta addabi sassan kasar da sama da kashi 80 cikin dari.
Gwamnatin Najeriya ta ce alkalummanta na shekarar 2025 sun nuna ana samun saukin hare-haren da ake kai wa da satar jama'a. "Yanzu ba a satar mutane kamar a baya da ake satar mutum sama da 200 lokaci guda," kamar yadda Abdul'aziz Abdul'aziz ɗaya daga cikin masu magana da yawun shugaban Najeriya ya shaida wa BBC.
Sai dai gwamnatin Birtaniya ta shawarci yan ƙasarta da su yi taka-tsantsan wajen tunanin yin balaguro zuwa sassan Najeriya.
Jihohin da gwamnatin Birtaniya ta yi gargaɗin a ƙauracewa a yankin arewaci, sun hada da Borno da Yobe Katsina da Zamfara da Adamawa da Gombe inda ta ce akwai babbar barazanar Boko Haram da Iswap a yankin arewa maso gabashi da kuma ƴanbindiga masu satar mutane a arewa maso yammaci.
Haka kuma, ta bayar da shawarar dakatar da duk wani balaguron zuwa Bauchi da Kaduna da Kano da Kebbi, Jigawa, Sokoto, Niger, Kogi, Plateau, da Taraba, da kuma gefen babban birnin tarayya Abuja sai idan ya zama dole.
An shawarci yan Birtaniya su taƙaita yawo a Abuja babban birnin Najeriya inda ta gwamnatin ta ce ana iya samun zanga-zanga da kuma hatsaniya da za ta iya haddasa tashin hankali
