A taron sasanci da aka gudanar tsakanin ƙananun hukumomin Charanci da Ɓatagarawa a cikin satin nan, an tsinkayo shugaban 'yan ta'addan a wani faifan hoto mai motsi yana cewa:
"Ku talakawa, idan kun tashi yin kuka, kar ku yi kuka da mu 'yan ta'adda. Ku yi kuka da shuwagabanninku, domin su suka so mu yi. Idan ba su so mu yi ba, ai ba mu yi. Kuma ai ga aya, yau sun kira mu so suke mu bari. Kuma da yardar Allah mun bari daga yau."Ya yi waɗannan kalaman ne a gaban dandazon al'umma da wakilan gwamnati waɗanda suka taru a filin sasancin.