Nijeriya Ta Samu Amincewar Gudanar da Cibiyar Ilimin Kafofin Yada Labarai Ta UNESCO Ta Farko

Kungiyar Ilimi, Kimiyya da Al’adu ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNESCO) ta amince da kafa Cibiyar Ilimin Kafofin Yaɗa Labarai ta Ƙasa da Ƙasa a Abuja, Nijeriya, a matsayin Cibiyar UNESCO ta Rukuni na Biyu, wacce ita ce irin ta ta farko a duniya.

Ibrahim Rabi'u

A wata sanarwa da Rabiu Ibrahim, Mai Taimaka wa Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai kan Harkokin Yaɗa Labarai, ya fitar a ranar Laraba, ya bayyana cewa UNESCO ta bayar da wannan muhimmiyar amincewa ne a Babban Taro na 43 na Hukumar Sadarwa da Bayanai da aka gudanar a birnin Samarkand na ƙasar Uzbekistan.

Cibiyar za ta kasance ne a hedikwatar Buɗaɗɗiyar Jami'ar Nijeriya (NOUN) da ke Abuja.

Ibrahim ya ce: “Da wannan amincewar, yanzu Nijeriya ta zama jagora a duniya wajen yaƙi da yaɗuwar labaran ƙarya a kafafen sada zumunta, tare da samun damar jagorantar bincike, tattauna manufofi da gina ƙwarewa a wannan muhimmin fanni na zamani.”

A jawabin da Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya gabatar a taron na UNESCO, ya bayyana wannan cigaba a matsayin “wata alamar yarda da girmamawa ga ƙasar mu.”

Ya tabbatar da cewa Nijeriya za ta ɗauki wannan nauyi da muhimmanci, inda ya bayyana cewa cibiyar za ta zama matattarar bincike da ilimi ta duniya domin taimaka wa jama’a da al’umma su iya tafiya cikin duniyar dijital cikin hankali da tabbaci.

Ministan ya ce: “Gwamnatin Nijeriya, ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ta himmatu wajen gina al’umma wadda ke ganin ’yancin faɗar albarkacin baki a matsayin ginshiƙin cigaban ƙasa. 

"Babban ginshiƙin wannan manufar shi ne bai wa kowa damar shiga fagen fasahar zamani, tare da ilimin kafofin watsa labarai a matsayin ginshiƙin cigaba.”

Ya bayyana cewa wannan nasara ta biyo bayan doguwar tafiya da ta faro tun a watan Oktoba 2022, lokacin da Nijeriya ta karɓi baƙuncin taron duniya na 10 kan Ilimin Kafofin Watsa Labarai a Abuja, inda ta yi alƙawarin kafa irin wannan cibiya ta UNESCO a ƙasar.

Ya ce: “Ina amfani da wannan dama in taya Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu murna bisa wannan nasara, wadda ke nuna jajircewar sa wajen ganin an cimma manufofin Shirin Sabunta Fata. Wannan nasara ce ba kawai ga Nijeriya ba, har ma ga nahiyar Afrika baki ɗaya.”

Ministan ya tabbatar da cewa Gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da aiki tare da UNESCO domin cika buƙatun cibiyar ta fuskar gina kayayyakin more rayuwa da kuma samar da ƙwararrun masana daga fannoni daban-daban domin tabbatar da nasarar wannan aikin.

Ya kuma bayyana cewa bikin ƙaddamar da cibiyar zai gudana ne a Fabrairu 2026 a Abuja, tare da halartar jami’an UNESCO, wakilan ƙasashe mambobi da abokan hulɗa daga sassa daban-daban na duniya.

Cikin tawagar da ta halarci Babban Taron na 43 na UNESCO domin shaida amincewar da aka bai wa IMILI Nijeriya a matsayin Cibiyar UNESCO ta Rukuni na Biyu, akwai Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa Kan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Sanata Injiniya Kenneth Eze; Shugaban Kwamitin Majalisar Wakilai kan Yaɗa Labarai, Ƙa’idoji da Halaye, Hon. Olusola Fatoba; Darakta-Janar na Hukumar Rediyon Tarayya (FRCN), Dakta Mohammed Bulama, wanda ya wakilci Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai; Darakta-Janar na Hukumar Talabijin ta Nijeriya (NTA), Malam Abdulhamid Salihu Dembos; Darakta-Janar na Hukumar Kula da Tallace-tallace ta Tarayya (ARCON), Dakta Olalekan Fadolapo; Darakta-Janar na Muryar Nijeriya (VON), Malam Jibrin Baba Ndace; da Jakadiyar Nijeriya a UNESCO, Dakta Hajo Sani, tare da wasu jami’an gwamnatin Nijeriya.

Post a Comment

Previous Post Next Post