Uwargidan tsohon shugaban kasa Shehu Shagari Ta Rasu Tana Da Shekara 89

Iyalan tsohon shugaban kasa na Najeriya, Alhaji Shehu Shagari, sun sanar da rasuwar uwargidansa ta ƙarshe, Hajiya Saratu Shehu Shagari, wacce ta rasu tana da shekara 89 a duniya.

A cikin wata sanarwa da ɗan marigayin shugaban kasa kuma Sarkin Mafaran Shagari, Kyaftin Bala Shagari, ya sanya wa hannu, ya bayyana cewa Hajiya Saratu ta rasu ne da misalin ƙarfe uku na rana a ranar Litinin bayan jinya mai tsawo.

Sanarwar ta ce: “Cike da alhini da jimami, muna sanar da rasuwar Hajiya Saratu Shagari, uwargidan tsohon shugaban ƙasar Tarayyar Najeriya, Alhaji Shehu Shagari, GCFR, Turakin Sakkwato.”

Kyaftin Bala Shagari ya bayyana mamaciyar a matsayin “abin koyi na ladabi, tawali’u da nutsuwa, wadda ta rayu cikin mutunci da kamala.”

Post a Comment

Previous Post Next Post