Hukumar Hasashen Yanayi ta Ƙasa (NiMet) ta bayyana cewa ana sa ran samun hazo mai ɗauke da ƙura da kuma ruwan sama mai haɗe da iska a wasu sassan ƙasar daga ranar Litinin zuwa Laraba, tare da gargaɗin jama’a su kasance cikin shiri da bin matakan kariya.
A cewar sanarwar da hukumar ta fitar ranar Lahadi a Abuja, an yi hasashen ƙaramin hazo mai ɗauke da ƙura a jihohin Katsina, Kano, Jigawa, Yobe, Borno da wasu sassan Kaduna a ranar Litinin, yayin da ake sa ran yanayi mai haske a sauran yankunan arewa.Hukumar ta ce a wasu sassan kudancin Taraba, ana iya samun ruwan sama mai iska a yammacin ranar, yayin da yankin tsakiyar ƙasar zai kasance da rana mai ɗan hazo da gajimare a wasu lokuta.
NiMet ta ƙara da cewa a wasu sassan Benue da Kogi ana iya samun ruwan sama a ƙarshen rana, yayin da yankin kudu gaba ɗaya zai kasance da gajimare da yiwuwar ruwan safe.
A cewar hasashen, ana sa ran ruwan sama a wasu sassan Ogun, Cross River, Akwa Ibom da Legas da safe, sannan a yammacin ranar ruwan zai yi yawa a wasu jihohin kudu maso yamma da kudu maso gabas.
A ranar Talata, hukumar ta yi hasashen yanayi mai haske da ɗan hazo a yankin arewa, tare da yiwuwar ruwan sama mai iska a kudancin Taraba da yamma.
Haka kuma, an ce jihohin Kogi, Benue da Kwara na iya fuskantar ruwan sama daga bisani.
A kudu, an yi hasashen gajimare da safe a jihohin Ogun, Legas da Cross River, sannan ruwan sama mai iska zai iya zuba da yamma.
Jihohin da lamarin zai fi shafa sun haɗa da Ogun, Edo, Enugu, Ondo, Abia, Imo, Ebonyi, Lagos, Cross River, Akwa Ibom, Rivers, Bayelsa da Delta.
A ranar Laraba kuma, NiMet ta yi hasashen rana mai haske a arewa da gajimare a tsakiyar ƙasa, inda ake sa ran ruwan sama mai iska a wasu wurare kamar Kwara, Benue da Kogi da yamma.
A kudu, ana hasashen gajimare da safe a Cross River, Rivers da Delta, sannan a yammacin rana ana sa ran ruwan sama mai ɗan karfi a wasu yankuna.
Jihohin Abia, Anambra, Imo, Ekiti, Osun, Ogun, Oyo, Ondo, Edo, Lagos, Bayelsa, Delta, Rivers, Cross River da Akwa Ibom na daga cikin wuraren da za su iya samun ruwan sama a yammacin Laraba.
Hukumar ta shawarci direbobi su yi taka-tsantsan yayin tuƙi a lokacin ruwan sama ko hazo saboda iya rage hangen hanya da ingancin iska, musamman a arewacin ƙasar.
Haka kuma ta shawarci masu ciwon asma da sauran cututtukan numfashi su guji fita yayin da hazo ko ƙura ke yawo.
NiMet ta kuma ja hankalin kamfanonin jiragen sama su nemi rahoton yanayi na filayen jirage kafin tafiya, don kauce wa jinkiri ko sauya jadawalin tashi saboda yanayi.
Hukumar ta buƙaci jama’a su riƙa bibiyar rahotanninta a shafinta na yanar gizo — www.nimet.gov.ng — da shafukan sada zumunta don samun sabbin bayanai kan yanayi.