Kasar China Ta Yi Fatali Da Barazanar Amurka Ga Najeriya

Gwamnatin kasar China ta bayyana adawa da barazanar da Amurka ta yi na kai hari a Najeriya, tana mai cewa irin wannan mataki zai iya haifar da rikici da tashin hankali a yankin Afirka ta Yamma da kuma barazana ga zaman lafiya a duniya.

CHINAMai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen China, Mao Ning, ta ce: “A matsayin Sin na abokiyar Najeriya a ɓangaren cigaba, China tana goyon bayan gwamnatin Najeriya wajen jagorantar jama’arta a kan tafarkin ci gaba da ya dace da yanayin ƙasarta. China tana adawa da duk wata ƙasa da ke amfani da addini ko haƙƙin ɗan Adam a matsayin hujja don tsoma baki cikin harkokin cikin gida na wasu ƙasashe, ko kuma yin barazana da takunkumi da amfani da ƙarfi.”

Tun da farko, shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar cewa Amurka na iya kaddamar da wani aikin soja a Najeriya don, a cewarsa, dakile abin da ya kira “cin zarafin Kiristoci” a kasar. Wannan magana ta jawo cece-kuce a fadin duniya, inda masana da masu lura da al’amura suka bayyana cewa barazanar Trump na da manufar siyasa da tasirin yanki, ba ta addini kadai ba.

Masana harkokin ƙasashen waje sun bayyana cewa matsayar China na nufin kare mutuncin Najeriya da cikakken ikon Afirka, tare da ƙalubalantar yunƙurin Amurka na kafa sansanin soja ko yin tasiri ta karfin iko a nahiyar.

Post a Comment

Previous Post Next Post