Shugaban Rasha, Vladimir Putin, ya bayar da umarni ga gwamnatin ƙasar da ta tsara cikakken tsarin (roadmap) don hako ma’adanan rare earths kafin watan Disamba.
Wannan umarni na zuwa ne a wani ɓangare na shirin Rasha na ƙarfafa tattalin arzikinta ta hanyar rage dogaro da ƙasashen waje wajen samar da muhimman ma’adinai da ake amfani da su wajen ƙera na’urori na zamani kamar wayoyi, kwamfutoci, da motoci na lantarki.
Putin ya jaddada cewa, ya zama wajibi a gaggauta kafa cibiyoyi da masana’antun cikin gida da za su kula da bincike, haƙowa, da sarrafa irin waɗannan ma’adanai don tabbatar da cewa Rasha ta tsaya da ƙafafunta a wannan fanni.
Masana na ganin wannan mataki zai ƙara ƙarfin tattalin arzikin Rasha da kuma matsayinta a kasuwar ma’adinai ta duniya, musamman ganin yadda ake samun karuwar buƙata ga irin waɗannan albarkatu.