Kamar yadda wani marubuci ya bayyana a shafinsa na Facebook "Ba don rashin kayan aikin zamani ba, da Janar Uba ya samu ceto. A lokacin da yake tuntuɓar dakarunsa ta WhatsApp, rundunar ba ta da na’urorin gano ainihin wurinsa kai tsaye. Don haka sai aka dogara ne da tattaunawar WhatsApp domin samun alamar wuri.
Idan dakarunmu suna da cikakkun na’urorin zamani, akwai yiwuwar wannan abin ba zai faru ba.
Abin lura shi ne: Janar ne—babban kwamanda a gaban yaƙi.
Ka yi tunani idan ƙaramin soja ne ke cikin irin wannan hali, ya za a kaya?
Gwamnatin Najeriya tana ƙoƙari, amma yana da muhimmanci a tabbatar sojojinmu sun samu duk kayan aikin da suka dace domin ƙarfafa tsaron ƙasa da kuma kare rayukan dakarunmu." In ji Adamu garba.
"Kwana biyu da suka wuce, Janar din Sojan yana hanyar dawowa tare da mayakansa daga wani farmaki da suka kai a dajin Sambisa, sai ISWAP suka musu kwanton bauna
Janar din Sojan ya samu damar tsallake harin kwanton baunar, ya tsere zuwa wani kauye dake kusa da gurin da suka yi harin, har ma ya samu damar yin magana ta WhatsApp ya sanar da cewa ya tsira yana cikin koshin lafiya
To sai labari ya karade media cewa an yi garkuwa da Janar din Soja, wannan ya jawo hankalin 'yan ta'addan ISWAP suka tsananta bincike, suka gano shi a kauyen, zai gudu suka harbe shi a kafa, bayan sun gama magana da shi sai suka hallaka shi
Wannan shi ne mafi girman barna da Media ta mana a Arewa, wato kai tsaye media ta taimaka wa 'yan ta'adda sun kashe mana Janar din Soja.
Mutanen da suke ba wa 'yan jaridu labarin abinda yake faruwa a fagen yaki da 'yan ta'adda ba karamin barna suke haifar wa ba a yaki da ta'addanci, lokaci ya yi da Gwamnati za ta dauki mataki mai tsanani a kan 'yan jaridun da suke saurin wallafa labarin da ya shafi yaki da ta'addanci ba tare da sahalewar Sojoji ba.
Mun rasa jarumin Soja, mai gaskiya, ma'abocin karatun Al-Qur'ani Mai girma, Sojan da ya ba wa mutanen yankin Damboa cikakken kariya daga harin 'yan ta'adda" Daga Datti Asalafy, kamar yadda ya bayyana a shafinsa na Facebook.
