Gidan tsohon ɗan majalisar tarayya, kuma tsohon ɗan takarar Gwamnan jihar Kaduna na jam'iyyar PDP, kuma Sarkin Bai Zazzau Alhaji Isah Ashirin Kudan ya kama da wuta ganga-ganga.
A jiya ne muka ga ɓullar wani faifan bidiyo yana yawo a social media, ɗauke da muryar tsohon ɗan majalisar yana bayanin irin yadda gidan yake ci da wuta, da kuma 'yan kayayyakin da suka tsira da su daga harin gibarar.
Gidan na Malam Isa da yake a Abuja ya ƙone ƙurmus a daren jiya sakamakon wutar da ta kama ganga-ganga, inda sai 'yan ƙalilan daga cikin kayan amfanin gidan aka samu aka tsira da su.
Sai dai sam barka, wutar ba ta yi nasarar halaka ko raunata ko da mutum guda ba, sai dai asarar dukiya da kayayyaki da aka yi.
Allah ya kiyaye gaba, ya mayar da mafi alheri.