Yayin da Najeriya ke fama da matsalolin tsaro a kusan duka sassan ƙasar, gwamnatin tarayyar ƙasar da na jihohi na yunƙurin ɗaukar matakan inganta tsaro domin kare al'ummominsu daga hare-hare.
Gwamnatin tarayya a nata ɓangare kan tura jami'an tsaro da kayan aiki zuwa yankunan da ake fama da rikice-rikicen.To sai dai a gefe guda kuma jihohin ƙasar, musamman waɗanda ke fama da matsalolin tsaro kan yi nasu ƙoƙarin domin inganta tsaron al'umominsu.
Kan haka jihar Legas da ke yankin kudu maso yammcin ƙasar ta kasance kan gaba wajen ɗaukar matakai da yin tsari na inganta tsaron al'ummarta, kamar yadda Dokta Kabiru Adamu shugaban kamfanin Beacon Security ya bayyana wa BBC.
Masanin tsaron ya ce jihar Legas ta ɓullo da wasu matakai huɗu na inganta tsaron yankunanta, wadanda suka haɗa da:
Samar da asusun tallafa wa tsaro, wanda kuma babu hannun gwamnatin jihar wajen gudanar da shi.
Ya ƙara da cewa jihar kuma na da tsarin amsa kiran gaggawa da tawagar kai ɗaukin gaggawa idan buƙatar hakan ta taso, sannan kuma tana da jami'an tsaron sa kai da ke aiki tare da sauran rundunonin tsaron gwamnatin tarayya.
Yankin arewacin Najeriya na fama da mabambantan matsalolin tsaro, kama daga matsalar Boko Haram da ISWAP zuwa ƴanbindiga masu satar mutane domin neman kuɗin fansa.
Jihohin yankin da dama sun yi ƙoƙarin ɗaukar matakan tsaro, domin kare al'umominsu.
Sai dai masana tsaro na ganin matakan da jihohin arewacin ƙasar ke ɗauka ba su da inganci, kuma akwai buƙatar su ƙara zage dantse domin inganta su.
Kan haka ne aka yi nazarin wasu matakai da wasu jihohin yankin suka ɗauka domin kare al'umominsu.
Jihohin yankin da dama sun yi ƙoƙarin ɗaukar matakan tsaro, domin kare al'umominsu.
Jihar Borno - wadda ke yankin arewa maso gabashin Najeriya - ta kasance jihar da ayyukan ƙungiyoyin Boko Haram da ISWAP suka fi muni.
Borno ta shafe kusan shekara 16 tana fama da hare-haren Boko Haram, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar dubban mutane tare da raba miliyoyi da muhallansu.
Daga cikin matakan ta jihar ta ɗaukar wa kanta domin tallafa wa jami'an tsaron gwamnatin tarayya aikin samar da tsaron jihar sun haɗa da:
- CJTF
Wata runduna ce ta musamman da ta ƙunshi matasa da magidanta da ke aiki tare da jami'an tsaro a jihar, kamar yadda Dokta kabiru Adamu ya bayyana.
''Babban aikin wannan runduna shi ne tattara bayanan sirri da tantance su, ta kuma taimaka wa jami'an tsaro wajen nuna musu hanyoyin shiga wasu garuruwa da ƙauyukan jihar,'' in ji shi.
Masanin tsaron ya ce wannan runduna ta CJTF ta kasance wata runduna abar koyi ga wasu jihohin arewacin ƙasar.
- Mafarauta
Baya da rundunar CJTF, gwamnatin jihar Borno ta yi ƙoƙari saka mafarauta cikin tsarin samar wa jihar tsaro.
''Rawar da mafarutar ke takawa na da matuƙar muhimmanci a tsarin tsaron jihar Borno, domin sukan taimaka wa jami'an tsaro da bayanan sirrin shiga kowane daji'', in ji shugaban na Beacon Security.
Jihar Zamfara da ke yankin arewa maso yammacin Najeriya ta kasance cikin johohin arewacin ƙasar da matsalar tsaro ta ƴanbindiga masu satar mutane domin neman kuɗin fansa ta yi wa katutu.
Gwamnatin jihar a matakinta ta yi yunƙurin samar da wasu hanyoyi na inganta tsaron al'ummar jihar.
Abubuwan da jihar ta yi ƙoƙarin yi sun haɗa da:
- Ƴan sa-kai
Wata runduna ce ta zaratan matasa da ke aikin samar da tsaro a faɗin jihar.
A wasu lokuta waɗannan jami'ai da aka sanya wa suna Askarawan Zamfara kan shiga yankunan da ƴanbindiga suke domin kai musu hari ko daƙile hare-haren ƴanbindigar, a cewar Kabiru Adamu.
- Asusun tallafa wa tsaro
Ita ma jihar zamfara kamar jihar Legas ta yi ƙoƙarin samar da wani asusu na musamman domin tallafa wa tsaron jihar.
Sai dai Kabiru Adamu ya ce a Zamfara gwamnatin jihar ce ke gudanar da asusun, saɓanin jihar Legas inda gwamnatin ta miƙa ragamar tafiyar da asusun ga ƴan kasuwa da masu zaman kansu.
Jihar yobe da ke arewa maso gabashin Najeriya na daga cikin jihohin arewacin ƙasar da suka yunƙura domin tallafa wa tsaronsu.
Yobe - wadda ta yi iyaka da jihar Borno na fama da hare-haren Boko Haram da ƴan ƙungiyar ISWAP.
Dokta Kabiru Adamu ya ce ita ma jihar ta ɓullo da matakai biyu da za a iya cewa na inganta tsaro ne a jihar da suka ƙunshi:
- CJTF
Kamar dai a jihar Borno mai maƙwabtaka, jihar Yobe ma ta samar da dakarun sibiliyan JTF, wato CJTF da ke taimaka wa jami'an tsaro wajen tattara bayanan sirri da kuma tantance su.
- Mafaruta
Masanin tsaro Kabiru Adamu ya ce jihar na amfani da mafarauta wajen taimaka wa jami'an tsaro sanin sirrin dazukan da mayaƙan Boko Haram da ISWAP ke ɓoye.
Jihar Plateau da ke yankin tsakiyar Najeriya na daga cikin jihohin ƙasar da ke fama da matsalar faɗan ƙabilanci da na rikicin manoma da makiyaya.
Mabambantan gwamnatocin jihar sun yi ƙoƙarin ɗaukar matakai da dama domin kare al'ummar jihar daga aukawa cikin rikice-rikice.
Kabiru Adamu ya ce ita ma jihar na da wani tsari na aiki da jami'an tsaro a matakin tarayya da nufin taimaka musu wajen samar da bayanan sirri.
Ya kuma ƙara da cewa jihar na da wata hukuma ta samar da zaman lafiya da ake yi wa laƙabi da ''Peace Commission'', wadda aikinta shi ne haɓaka zaman lafiya tsakanin al'ummar jihar.
Kamar jihar Filato mai maƙwabtaka, Benue na daga cikin jihohin Najeriya da suka yi ƙaurin suna wajen faɗan ƙabilanci da na manoma da makiyaya.
''Ita ma tana da tsarin da ke ƙarfafa wa tsaronta, kuma suna taimaka mata ba laifi'', a cewar Kabiru Adamu.
Ya ƙara da cewa jihar na da hukumar wanzar da zaman lafiya wato ''Peace Commission'', kamar dai a jihar Filato.
Masanin tsaron ya kuma ce jihar na da ƴan sa-kai da ke aiki da jami'an tsaro, a wasu lokutan kuma suke tabbatar da zaman lafiya da kansu.
Kabiru Adamu ya kuma ce jihohi irin su Kaduna da Neja su ma suna da makamancin wannan tsari.
Dokta Kabiru Adama ya ce wani mataki da kusan duka jihohin yankin suka ɗauka domin magance tsaron jihohinsu shi ne, samar da kwamishinonin tsaron cikin gida, ko kuma naɗa mai bai wa gwamna shawara kan sha'anin tsaro.
''Wannan abin a yaba musu ne, kuma sun yi ƙoƙari kan hakan''.
Sai masanin tsaron ya ce akwai tantama game da ƙwarewar waɗanda ake naɗawar a waɗannan muƙaman.
''Galibi za ka taras yawancinsu tsoffin jami'an sojoji ko na ƴansanda, waɗanda kawai ƙwarewar aikin tsaron suke da ita, amma ba su da ƙwarewar tsarin tsaro, musamman a matakin jiha'', in ji shi.