Shahararren Mawakin Zamani Na Afrobeat, Burna Boy Ya Koma Addinin Muslunci

 Kamar yadda shafukan jaridun kafar Fezbuk suka rawaito, shahararren mawaƙin nan ɗan asalin ƙasar Nijeriya da ya shahara a fagen waƙoƙin zamani na Turanci, ya karɓi addinin muslunci, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce ga wasu al'umomi a fadin kasar.

Burna Boy

Damini Ebunoluwa Ogulu (Burna Boy) an haife shi ne a jihar Port Harcourt, Nigeria a shekarar 1991. Kuma ɗaukakarsa ta fara ne tun shekarar 2012 yayin da ya saki wata waƙarsa mai suna "Like To Party" wacce ta zagaye ko'ina a duniyar mawaƙan Afrobeat. Ogulu ya ƙara tsunduma cikin harkokin waƙoƙin zamani sosai musamman lokacin da ya dawo daga ƙasar Ingila, inda can ne ya yi karatu tun lokacin yana ɗan kimanin shekaru 20.

Ogulu ya samu goyon baya sosai daga mahaifiyarsa a wajen harkokinsa na waƙoƙin zamani, wadda daga baya ta kasance manajarsa a fagen. Ogulu ya bayyana cewa ya daɗe yana sha'awar addinin muslunci, kuma ya bayyana cewa a kodayaushe yakan yi bincike game da addinin, wanda daga ƙarshe ya yanke shawarar sauya sheƙa daga kiristanci zuwa addinin Islama.

Post a Comment

Previous Post Next Post