Shugaban Amurka Donald Trump ya umarci sojojin kasarsa su kasance cikin shirin ko-ta-kwana game da yiwuwar far wa ƙungiyoyin "ƴan ta'adda" da ya ce suna yi wa Kiristoci kisan gilla a Najeriya, "kuma gwamnati ba ta ba su kariya ba".
Trump bai faɗi kisan gillar da aka yi ba amma kuma zargin kisan ga mabiya addinin Kirista a Najeriya na ci gaba da jan hankali a tsakanin wasu ƴan jam'iyyar Republican a Amurka.Ƙungiyoyin da ke sanya ido kan rikice-rikice sun ce babu wata shaidar da ke nuna cewa ana kashe Kiristoci fiye da Musulmi a Najeriya, inda suka ce hare-haren ƴan ta'addar na shafar dukkan ɓangarorin biyu ne.
Haka nan gwamnatin Najeriya ta yi watsi da iƙirarin yi wa Kiristoci "kisan ƙare-dangi", tare da bayyana cewa Najeriya na maraba da duk wani matakin taimaka mata wajen daƙile ayyukan "ƴan ta'adda".
Sai dai babban abin da ya fi ɗaukar hankali game da wannan batu shi ne yadda shugaban Amurkar ya nuna cewa abu ne mai yiwuwa Amurka ta iya ɗaukar matakin soji kan Najeriya, ƙasar Afirka mafi yawan al'umma kuma mai ɗimbin arziƙin man fetur.