Tsohon ɗantakarar shugaban Najeriya a Jam'iyyar Labour Peter ya ce barazanar Shugaban Amurka Donald Trump kan tura sojojin ƙasarsa su yaƙi ta'addanci, da ma sanya ƙasar a cikin waɗanda yake sa ido a kansu abin damuwa ne da ɗaga hankali ga dukkan 'yan ƙasar.
Obi ya bayyana haka ne a shafinsa na X, inda ya ce dukkan ɗan Najeriya mai son ƙasar dole abin da faruwa ya ja masa hankali.
"Babu shakka Najeriya na fama da matsalar tsaro, wadda ta yi sanadiyar mutuwar mutane da dama da ma asarar dukiya. Ƙungiyar Amnesty ta ruwaito cewa aƙalla mutum 10,000 aka kashe a Najeriya daga watan Mayun 2023, kuma kamar yadda na sha nanatawa, kashe-kashe a Najeriya abin takaici ne, kuma abin Allah-wadai da ya zama dole a tashi haiƙan wajen magancewa."
Obi ya ce za a iya magance matsalar ta hanyar samun shugabanci na nagari, "duk da cewa ba a wannan gwamnatin matsalar ta fara ba, amma akwai rashin ƙwarewa da rashin takaɓus daga ɓangaren wannan mulkin na gwamnatin APC wajen tunkarar matsalolin tsaro da ƙasar ke fuskanta."
Ya ce Najeriya da Amurka suna da tarihin alaƙa da juna mai kyau, "kuma bai kamata a watsar da wannan alaƙar ba a yanzu. Wannan sabuwar dambarwar na buƙatar haɗakar diflomasiyya da tattaunawa tsakanin ƙasashen biyu domin lalubo hanyoyin magance matsalar."
