Hukumomin Isra’ila sun kama wani tsohon lauya na rundunar soji bayan da wani bidiyo ya bayyana a intanet yana nuna sojojin Isra’ila suna cin zarafi da dukan wani ɗan Falasɗinu da suke tsare da shi.
Bidiyon, wanda ya bazu cikin sauri a kafafen sada zumunta, ya nuna yadda wasu sojojin Isra’ila suka doki mutumin sannan suka yi masa ba’a, yayin da yake a hannunsu a matsayin wanda aka kama. Wannan hoton ya jawo fushin wasu ƙasashen duniya da kungiyoyin kare haƙƙin bil’adama, suna neman a gudanar da cikakken bincike da hukunta masu laifi.
Rahotanni daga kafafen yaɗa labarai na Isra’ila sun ce tsohon lauyan soja ne ake zargi da bada bidiyon ga kafafen yaɗa labarai, lamarin da rundunar sojin Isra’ila ta bayyana a matsayin “babbar ɓarnar tsaro.”
A cikin wata sanarwa, rundunar sojin Isra’ila (IDF) ta ce tana gudanar da cikakken bincike kan lamarin, tare da bayyana cewa irin wannan hali “ba ya nuna ɗabi’u ko ƙa’idojin rundunar IDF.”
A nasa bangaren, jami’an Falasɗinu sun la’anci cin zarafin, suna mai cewa wannan al’amari yana nuna irin zaluncin da Isra’ila ke yi wa al’ummar Falasɗinu, tare da kira ga kasashen duniya su shiga tsakani don tabbatar da adalci.
Kama tsohon lauyan ya sake tayar da muhawara game da ‘yancin faɗar albarkacin baki da kuma kare masu tona asiri (whistleblowers) a cikin tsarin tsaro na Isra’ila.