Shugaban Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa ya ce za a gudanar da bincike kan wani jirgi da aka yi shatarsa zuwa ƙasar ɗauke da Falasɗinawa fiye da 150 daga Gaza.
Falasɗinawan, da suka haɗa da iyalai da ƙananan yara, ba a ba su damar yin bulaguron na tsawon sa'a 10 zuwa ƙasar ba, sakamakon rashin sahihin hatimi a kan takardun izininsu.An dai ba su damar zama a ƙasar ne bayan shiga tsakani da wata ƙungiyar bayar da agaji ta yi.
23 cikin mutunen sun fice daga ƙasar zuwa wasu ƙasashen yayin da sauran suka zauna a ƙasar.
Kawo yanzu ba a san yadda suka baro Gaza ba.
Hukumomin Isra'ila sun ce mutanen sun fice daga Gaza ne bayan samun amincewar wata ƙasa ta daban.
To amma ba ta fayyace sunan ƙasar ba.