Babbar kotun tarayya a Najeriya ta umarci jam'iyyar adawa ta PDP ta bai wa tsohon Gwamnan Jigawa Sule Lamido damar shiga takarar shugabancin jam'iyyar.
Kafofin yaɗa labarai sun ruwaito Mai Shari'a Peter Odo Lifu na cewa kuskure ne PDP ta hana Lamido damar sayen tikitin takarar.Baya ga haka, kotun ta umarci PDP ta dakatar da taron na Asabar saboda gazawa wajen wallafa jadawalin taron a kan lokaci domin sanar da 'ya'yanta kamar yadda dokar zaɓe ta tanada.
Wannan ne umarnin kotu na uku da ke hana PDP yin taron, wanda zai ba ta damar zaɓen sababbin shugabanni a mataki na ƙasa.
Sai dai jam'iyyar ƙarƙashin jagorancin Umar Ilya Damagun ta ce ba za ta fasa ba saboda ita ma akwai ktoun da ta bayar da umarnin ta ci gaba da shirin gudanar da taron.