Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya tsawaita wa'adin Buba Marwa a matsayin shugaban hukumar NDLEA mai yaƙi da Sha da fataucin kayan maye a ƙasar.
Cikin wata sanarwa da fadar shugaban ƙasar ta fitar a ranar Juma'a, ta ce Shugaba Tinubu ya amince da da ƙarin wa'adin shekara biyar ga Buba Marwa.Tsohon shugaban Najeriya, Marigari Muhammadu Buhari ne ya fara naɗa Buba Marwa a watan Janairun 2021.
Amincewa da tsawaita wa'adin Marwa - wanda tsohon gwamnan soji na jihohin Lagos da Borno ne - na nufin zai kasance shugaban hukumar NDLEA har nan da 2031.