Dan majalisa mai wakiltar Mazabar Agwara/Borgu, Hon. Jafaru Mohammed Ali, ya tsira daga harin 'yan bindiga bayan da ‘yan bindigar suka bude wa tawagarsa Wuta yayin da yake ziyarar mazabarsa ranar Talata. Sojoji shida dake yi masa rakiya don ba da tsaro ga tawagar tasa duk sun mutu a yayin harin.
An ce ‘yan bindigar fiye da 50, suna dauke da muggan makamai masu sarƙaƙƙiya kuma sun yi wa ayarin dan majalisar kwanton bauna a ƙauyen Kuble da ke kan hanyar Babanna. Dan majalisar da ma’aikatansa farar hula sun tsira ba tare da wani rauni ba a lokacin harin.
Lamarin ya faru ‘yan mitoci kadan daga Kainji National Park, inda ‘yan bindiga suka karɓe iko kuma suka mamaye kusan shekaru biyu yanzu. Daga baya, an tseratar da dan majalisar da sauran tawagarsa zuwa garin Babana bayan da sojoji suka aika da ƙarin rundunar jami'ai zuwa wurin.
Wani ɗan ƙauyen ya ba da sanarwar cewa, Gwamna Mohammed Bago ya tura jirgin sama zuwa Babanna don ɗauko dan majalisar da sauran tawagarsa zuwa Minna don tabbatar da tsaro.
An samu labarin cewa ana ci gaba da sa ido kan tsaro da lura da bayanai a fadin yankin Kuble–Babanna–Wawa don bin diddigin waɗanda suka aikata laifin da kuma tabbatar da tsaron duk ma’aikata da al’ummomin da ke cikin yankin dajin.
