Hukumar Shige da Fice ta Najeriya (NIS) ta sanar da shirinta na ƙaddamar da takardar tafiya ta gaggawa (Single Travel Emergency Passport – STEP), wacce za ta kasance sabuwar takardar tafiya mai ɗauke da bayanan yatsa (biometric) domin taimaka wa ’yan Najeriya da ke ƙasashen waje waɗanda fasfonsu suka ƙare, ko suka ɓace ko aka sace, su koma gida cikin aminci da tabbaaci.
Babbar Kwamptrola ta Hukumar, Kemi Nanna Nandap, ce ta bayyana haka a yayin taron haɗin guiwar jigo na Khartoum, Rabat da Niamey Processes da aka gudanar a Abuja, wanda Najeriya ta shirya tare da gwamnatin Faransa.Wannan na cikin wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na Hukumar, ACI Akinsola Akinlabi, ya fitar a ranar Laraba.
A cewar Nandap, wannan sabon tsarin STEP zai maye gurbin takardar tafiya ta gaggawa da ake amfani da ita yanzu wato Emergency Travel Certificate (ETC), a wani ɓangare na ci gaba da sauye-sauyen da Hukumar ke yi domin ƙarfafa tsarin tantancewa da kula da iyakoki bisa ƙa’idar ƙwararrun ƙasashe.
Ta ce: “STEP za ta zama takardar tafiya ta wucin gadi ga ’yan Najeriya da ke ƙasashen waje waɗanda fasfoforsu suka ƙare, suka ɓace ko aka sace, domin ba su damar komawa gida cikin tsaro da tabbatarwa.”
Nandap ta ƙara da cewa za a fitar da takardar a jakadun Najeriya da ofisoshin jakadanci na ƙasashen waje, kuma za ta kasance mai amfani sau ɗaya kacal, abin da ke nuna jajircewar Hukumar wajen samar da ingantaccen sabis da kuma kare bayanan ɗan ƙasa.
Taron ya haɗa manyan masu ruwa da tsaki a harkar kula da ƙaura da tsaro, ciki har da Hukumar ’Yan Gudun Hijira, ’Yan Gudun Ciki da Masu Hijira (NCFRMI), NAPTIP, ECOWAS, AU, EU, da wakilai daga ƙasashen Afirka da Turai.
Taron matakin ƙoli ya mayar da hankali kan ƙarfafa haɗin guiwa wajen yaki da safarar ’yan sida fataucin mutane, tare da ba da muhimmanci ga rigakafi, kariya da gurfanar da masu laifi a hanyoyin ƙaura na yankuna daban-daban.
A cikin jawabinta na musamman mai taken “Insights on Prevention and Protection as Strategic Pillars to Effective Law Enforcement and Prosecution Responses,” Nandap ta fayyace ajandar sauye-sauyen hukumar wacce ke nufin inganta tsarin kula da ƙaura, haɗin gwiwar ƙasa da ƙasa, da kuma gina ƙwarewar ma’aikata.
Sanarwar ta ƙara da cewa, “Babbar Kwamptrola ta tabbatar da cewa Najeriya za ta ci gaba da kasancewa cikin tattaunawar ƙasa da ƙasa kan harkokin ƙaura, tare da tabbatar da cewa Hukumar Shige da Fice za ta ci gaba da daidaita manufofinta da ayyukanta da ƙa’idodin duniya domin tabbatar da tafiya cikin tsari, tsaro da doka.”