Femi Falana Ya Bukaci Gwamnatin Tarayya Ta Karyata Labarin Karya Na “Kisan Gilla Ga Kiristoci” A Najeriya

Lauyan kare haƙƙin ɗan Adam, Femi Falana (SAN), ya shawarci Gwamnatin Tarayya da ta ɗauki matakan gaggawa domin ƙaryata abin da ya kira “labarin ƙarya” na kisan gilla ga Kiristoci a Najeriya, yana mai gargaɗin cewa shiru daga ɓangaren gwamnati yana ƙara hura wutar yaɗa bayanan ƙarya a ƙasashen waje.

Da yake magana a shirin Politics Today na tashar Channels Television, Falana ya bayyana cewa kamfen ɗin da ke yaɗa zargin ana kashe Kiristoci da gangan a Najeriya yana tafiya ne tsawon shekaru ba tare da wasu sahihan martani daga gwamnati ba.

“A cewar Farfesa Jibrin Ibrahim, masani kuma mai mutunci, wannan yaɗa labarin kisan Kiristoci a Najeriya yana gudana ne tsawon shekaru takwas ba tare da wani ƙalubale daga gwamnati ba,” in ji Falana. “Wasu sukan tafi Amurka, su dawo, su ci gaba da yaɗa wannan labari ba tare da jami’an gwamnati sun ce komai ba.”

Falana ya ce, maimakon gwamnati ta mayar da martani cikin fushi ga kalaman tsohon shugaban Amurka, Donald Trump, ya kamata ta duba kura-kuran cikin gida da suka ba wa irin waɗannan ra’ayoyi damar yaɗuwa.

“Maimakon mu damu da kalaman Trump, ya kamata mu tambayi kanmu inda muka yi kuskure. Wani dole ne ya faɗi gaskiya,” in ji shi.

Falana ya jaddada cewa masu aikata ta’addanci a wasu sassan ƙasar ba addini ke motsa su ba, sai dai buƙatar mallakar ƙasa da kiwon dabbobi.

“Ba addini ke sa su kashe mutane ba,” in ji shi. “Suna kashewa ne don su faɗaɗa ƙasa, don kiwo. Matsalar tana ci gaba ne saboda har yanzu ana barin kiwon dabbobi a fili duk da cewa Majalisun Gwamnonin Arewa da Kudanci sun amince da haramta kiwon a fili.”

Ya zargi gwamnati da rashin aiwatar da yarjejeniyar, yana nuna cewa ana ci gaba da kiwo a fili har ma a babban birnin tarayya.

“A hanyata zuwa Abuja jiya, na ga shanu a kan titin filin jirgin sama. Najeriya ce kaɗai ƙasar da irin haka ke faruwa. Har ma za ka ga shanu suna kiwo a gefen hanyar Majalisar Dokoki ta Ƙasa,” in ji shi.

Falana ya bayyana cewa gina ranch (wuraren kiwo na zamani) shi ne mafita ta gaskiya ga rikicin manoma da makiyaya, amma ya zargi gwamnati da ƙungiyoyin makiyaya da hana aiwatar da tsarin.

“A ƙasashen da suka ci gaba, akwai wuraren kiwo da aka kulle inda ake samar da ciyawa da ruwa. Har ma ‘ya’yan makiyaya na zuwa makaranta a wurin. To, me ya sa gwamnati da ƙungiyar Miyetti Allah ke ƙin kafa irin waɗannan wurare a fadin ƙasa?” ya tambaya.

Lauyan ya kuma nuna damuwa kan ƙarin yawaitar sace mutane da kuma gazawar hukumomin tsaro wajen amfani da fasaha domin gano masu aikata laifin.

“Ta yaya za a ce ƙasa mai mulki ta zamani tana barin ‘yan ta’adda su kashe jama’a ba tare da wani yunƙurin gano su ba?” in ji Falana.

“A yau, fasaha ta kai matakin da duk inda aka yi kiran waya za a iya gano shi. Amma iyalan waɗanda aka sace su ke tara kuɗin fansa, maimakon jami’an tsaro su bi sahun ‘yan ta’addan.”

Falana ya ce ci gaba da biyan kuɗin fansa yana ƙara sa satar mutane zama sana’a mai riba.

“Da zarar an tuntubi iyalan wanda aka sace, ‘yan sanda su ya kamata su fara aiki ba su jira a kawo kuɗin fansa ba. Idan ba haka ba, satar mutane za ta zama kasuwanci, shi ya sa muka shiga matsala,” ya gargadi.

A ƙarshe, Falana ya buƙaci Gwamnatin Tarayya ta kare mutuncin ƙasa da kanta a idon duniya.

“Mu ne muka jawo wannan kunya da kanmu a matsayin al’umma. Ana kallonmu kamar mulkin mallaka ne na Amurka. Ba ma iya maida martani ga Trump  ta yaya hakan zai yiwu? Ina wannan munafurci ya samo asali?” in ji shi.

Post a Comment

Previous Post Next Post