Sojojin Nijeriya Sun FadaTarkon Mayakan ISWAP

Ayarin wasu sojojin Nijeriya ya faɗa a tarkon kwanton ɓaunan mayaƙan ISWAP a daren Juma’a a Jihar Borno. Rahotanni na nuna cewa mayaƙan sun yi garkuwa da Janar ɗin tare da hallaka sojoji da dama da ke tare da shi, ciki har da mambobin CJTF.

Sojojin Nijeriya

Rahoton kafar HumAngle, cibiyar da ke mayar da hankali kan rikice-rikice da batutuwan jin ƙai, wanda PremiumTimes ta ruwaito, ya ce Janar ɗin da aka yi garkuwa da shi shi ne kwamandan wani bitget ɗin soji, kuma shi ne yake jagorantar dakarun a lokacin.

Idan ta tabbata, “wannan shi ne karo na farko da wata ƙungiyar ta taɓa kama wani Janar da ke kan aiki a fagen daga,” a cewar HumAngle.

Duk da cewa ’yan ta’adda sun kashe manyan jami’an soja a wasu hare-hare, amma ba kasafai ake samun labarin garkuwa da jami’an soja masu muƙami irin wannan ba.

Har yanzu hukumomin soji ba su fitar da sanarwa kan lamarin ba, kuma ba a tabbatar da adadin waɗanda suka mutu ba.

Kakakin Rundunar Sojin Najeriya, Laftanar-Kanar Onyechi Anele, bai amsa sakon tambaya da aka tura masa kan lamarin ba.

Post a Comment

Previous Post Next Post