Gwamnatin Taliban ta Afghanistan ta zargi Pakistan da rashin yin abun da ya dace bayan tattaunawar zaman lafiya tsakanin ƙasashen biyu.
Mai magana da yawun Taliban ya bayyana cewa Pakistan ba ta nuna gaskiya da natsuwa wajen tattaunawar da aka yi ba, wanda hakan ya sa ƙoƙarin kawo ƙarshen tashin hankali a yankin ya rushe.
Taliban ta ce tun bayan da ta karɓi mulki a 2021, ta yi ƙoƙarin ƙarfafa dangantaka da makwabta, amma Pakistan ta ci gaba da yin zarge-zarge kan cewa mayaƙan da ke kai hare-hare a yankinta suna samun mafaka a Afghanistan.
Sai dai Pakistan ta mayar da martani, tana cewa Taliban ba ta ɗauki matakan hana ‘yan ta’adda da ke tsallakawa daga ƙasarta ba, lamarin da ke barazana ga tsaron ƙasarta.
Masana harkokin diflomasiyya sun bayyana cewa wannan saɓani tsakanin ƙasashen biyu na iya ƙara tsananta rikicin yanƙin, tare da rage zaman lafiya a yankin Asiya ta Tsakiya.