Tarayyar Turai Ta Rage Kudirin Ta Na Rage Dumamar Yanayi Kafin Taron COP30 a Brazil

  Tarayyar Turai (EU) ta amince da sabon tsarin da zai rage  ƙudirin ta na yaƙi da ɗumamar yanayi, a wani mataki na ƙarshe kafin babban taron COP30 da za a gudanar a ƙasar Brazil.

Dumamar Yanayi

Sabuwar yarjejeniyar da aka cimma bayan doguwar muhawara tsakanin ƙasashen membobinta ta sanya burin rage fitar da hayaki mai gurɓata muhalli da kashi 85 zuwa 90 cikin 100 kafin shekarar 2040, idan aka kwatanta da burin kashi 90 cikin 100 da hukumar Tarayyar Turai (European Commission) ta gabatar tun da farko.

Masana sun bayyana cewa wannan sassauci ya samo asali ne daga wasu ƙasashen EU da ke dogaro da man fetur da iskar gas, waɗanda ke fargabar illar tattalin arziki idan aka tsaurara matakan kare muhalli.

Ƙungiyoyin kare muhalli sun soki wannan mataki, suna cewa EU ta koma baya kan alƙawuran ta, lamarin da zai iya rage ƙoƙarin duniya na daƙile ɗumamar yanayi zuwa digiri 1.5°C.

Wannan yarjejeniya ta zo ne kafin zuwan shuwagabannin duniya zuwa Brazil domin taron COP30, inda za a tattauna sabbin tsare-tsare na rage hayaƙi da kuma batun kuɗaɗen tallafin kare muhalli.

Sai dai duk da wannan koma baya, jami’an EU sun jaddada cewa har yanzu suna da niyyar ci gaba da zama jagora a yaki da sauyin yanayi, duk da ƙalubalen siyasa da tattalin arziki da suke fuskanta a gida.

Post a Comment

Previous Post Next Post