Ga Abinda Ya Rubuta A Shafinsa Na Fezbuk
"Duk wanda zai ce yana da sabanin fahimta da Sheikh AbdulJabbar ba zai kai ya mu ba, kuma duk mai sukansa akan ra'ayoyinsa da koyarwarsa ba zai kai ya mu ba, wannan kuwa yafi rana bayyana, sai dai mu iyakar Sabanin fahimta da bambancin ra'ayoyi shine tsakanimmu dashi ba kiyayya.
Amma idan za'a yi magana ta tsakani da Allah wasu dama akwai hassada da kiyayya da sukayi tasiri a zukatansu wanda suka tunkudasu izuwa dafawa abinda sukayi a hakkinsa kuma yanzu sun samun makanta har suna cewa basu ga wata fuska ta zalunci da ake yiwa Malam AbdulJabbar ba.
Tun asali ambaton kalaman Malam AbdulJabbar da Zagin Manzon Allah (saw) shine babban zaluncin farko domin akwai Bambanci tsakanin munana ladabi bisa kuskure da munana Ladabi bisa ganganci da kuma Zagi.
Idan akwai rikitarwa to za'a iya samunta a biyun can na farko amma shi zagi babu wani rikitarwa ciki kowa yasan kalaman zagi, amma haka aka ringa nasabta masa zagi ana sane.
Bayan nan aka shirya Mukabala aka ce za'a bayar da isasshen lokaci ya kare kansa, daga baya aka shirya mukabala irinta mintuna, aka sauka daga kan fikirorinsa aka koma tuhumar lafuzza da Usulubin koyarwa.
Sannan aka dauko dan Izala ya zamo Alkali a mukabalar, wanda sam sam bai daceba Kuma ba Adalci bane, karshe suka rubuta cewa wai ya kasa kare kansa.
Gwamnati ta kamashi ba tare da wani shiri ba kamu irin na yaudara ba bisa doka ba Kuma Gwamnati ta gurfanar dashi gaban kotu, akayi ta jan Shari'ar tukunna akace aje a kasheshi ta hanyar rataya.
Sannan bayan wannan kotu ta yanke masa wani irin hukunci na kisa, kuma ta siga da bashida wani asasi a littafin Allah ko Sunnar Manzon Allah (saw) tare da cewa kowa yasan bai aikata abinda ake tuhumarsa ba koda kuwa yana yin kuskure a ta'abiri da tashbihi.
Sannan aka bayar da damar ya daukaka kara kuma aka je aka hana Shari'ar ta cigaba da tafiya.
Amma tare da haka wai Malami yake bude baki yace ba'a zalunci AbdulJabbar ba tare da cewa kwatan irin wadannan zalunci da aka yiwa Sarkin gida idan dan Team dinsa aka yiwa sai yafi kowa zagi da tsinuwa da nuna kiyayya ga Gwamnatin da ta jagoranci yin haka.
Abinda muke gayawa Gwamnatoci su sani mufa ba Jahilai bane mun karanta doka kuma mun fahimci Dokokin dake kunshe cikin kundin tsarin mulkin kasar nan.
A wacce doka aka hana Mutum yancin yin ra'ayinsa a Addini a duk fadin duniya?
Hasalima abinda yasa muke mutunta tsarin democracy kenan yadda ya baiwa kowa damar yayi ra'ayinsa da fahimtarsa, to idan haka ne kuwa da wanne dalili aka bar masu bautar wanin Allah suna Addininsu yadda suka ga dama amma a kama Malami akan ra'ayinsa ace aje a kasheshi sabida rai bashida darajar komai a wajenku.
Maganar gaskiya Saba'in da Biyar 75 % cikin dari na Malamai ba su da wayewar da muke da ita ta yadda duk zafin sabani muke iya tsayar da ita a magana ta fatar baki ba tare da shiga hurumin abokin sabanin ba koda ta nahiyar Mutuncinsa ne ballantana Jininsa.
Amma ba zamu zura ido muna ganin ana cin mutuncin Malaman Musulunci da sunan bawa Aqida kariya ba , kuma indai muna raye muna numfashi babu wani Malami matukar ba dan ta'adda bane da zamu zuba ido a kamashi ana zaluntarsa irin haka.
Malam AbdulJabbar yana fuskantar zalunci karara kuma inshaallah karshen wannan zalunci yazo da yardar Allah zai yi free a kurkusa,
Yau Laraba 20 November 2025 na je wata Unguwa a Abuja inda na biyo ta kuje kuma na shiga Kurkukun kuje din inda ake tsare da Malam AbdulJabbar sai dai ban samu ganinsa ba sabida banje a Lokacin visiting ba.
Ala ayyi halin ni ko Yahya masussuka da muke kan fama dashi sabida Aqidunsa a yanzu bana tare da duk wani shiri na cutar dashi koda kuwa hana masa yancin wa'azi ne , domin da Fikra ake magance Shubha amma ba da karfin Gwamnati ba.
Kirana izuwa Gwamnatoci a dukkan matakai shi ne ku ji tsoron Allah ku saki bawan Allah Malam AbdulJabbar ya koma cikin iyalinsa, sannan ku nisaci shiga fitintunu irin wannan a nan gaba.
Allah ka gaggauta bayar da mafita gareshi muna Addu'ar Allah ka gaggauta kubutar dashi Alfarmar Sayyaduna Rasulullahi (saw)."
AbdulAziz Tal'udiy Haidara
20 November 2025

