Gwamnatin Tarayya Ta Tura Tawaga Zuwa Amurka Kan Zargin “Kisan Kirista” A Najeriya

Gwamnatin tarayya ta tura tawaga zuwa Ƙasar Amurka domin tattaunawa da jami’an gwamnatin Amurka kan zarge-zargen da ake yi na “kisan Kirista” a Najeriya.

Tawagar, wadda Mai Baiwa Shugaban Kasa Shawara kan Tsaro, Mallam Nuhu Ribadu, ke jagoranta, za ta gabatar da bayanai, ta bayyana muhimman alkaluman tsaro, tare da tabbatar da aniyar Najeriya na kare ’yancin addini da kuma kare rayukan dukkan ’yan kasa ba tare da bambanci ba.

A cikin tawagar akwai ƙaramin Ministan Harkokin Waje, Ambasada Bianca Ojukwu; Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Kayode Egbetokun; Babban Lauyan Gwamnati, Lateef Fagbemi, SAN; Hafsan Hafsoshin Tsaro, Janar Olufemi Olatunbosun Oluyede; Daraktan Leken Asiri na Rundunar Tsaro, Lt. Janar E.A.P. Undiendeye; Mashawarciyar NSA kan Tsare-tsare, Ms. Idayat Hassan; Daraktan Huldodin Ƙasashen Waje na ONSA, Ambasada Ibrahim Babani; Mai riƙe da mukamin Chargé d’Affaires na wucin gadi a Washington D.C., Ambasada Nuru Biu; da kuma Mista Paul Alabi na ofishin jakadancin Najeriya a birnin.

Tawagar za ta gana da jami’an gwamnatin Amurka, ’yan majalisa, da ƙungiyoyin manufofi domin magance damuwa, kawar da bayanan da ba daidai ba, tare da ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro tsakanin kasashen biyu.

Bayan kammala aikin, tawagar za ta mika rahoton bincike da shawarwarinta ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Post a Comment

Previous Post Next Post