Kamar yadda Sheikh Ibrahim Musa Faskari ya wallafa a ranar Jumma'a, 21/11/2025 a shafinsa na Fezbuk, shehun malamin ya bayyana jerin tuhumar da al'ummar musulmi ke yi wa Yahaya Masussuka dangane da da'awarsa ta kur'ani zalla a fadin Nijeriya. Ga tuhumar da ya wallafa
1. Ya ce hadithai suna ƙaryata ayoyin Alkur'ani. Muna son a TITSIYE shi ya kawo dalilai da suke tabbatar da haka.
2. Yace: HADITHAI BA MAGANGANUN ANNABI (SAW) ba ne. A tambaye shi ya kawo mana maganganun Annabin na gaskiya, in kuma Annabin ba ya magana, shi ma sai ya faɗi, in kuma Annabin ya yi magana amma duk maganganun sun ɓace a tsawon tarihi, shi ma ya faɗi domin kowa ya gane.
3. Yace: Bukhariy da Muslim duk maƙaryata ne kuma ƴan giya ne. Ya zo ya kawo shaidar in da suka sha giya, kuma ya bayyana inda su ka yi ƙaryar.
4. Yace: Annabi (SAW) ba zai yi ceto ba, a zaunar da shi a tabbatar masa da ceton Annabin rahama.
5. Yace: Salloli biyar ba ruwaito su aka yi ba, gado su aka yi daga zamani zuwa zamani. A tsare shi ya faɗi shi a wurin wa ya gada, kuma menene bambancin haka da ISNADIN HADITHI?
6. Yace: a tarihi babu wata Nana Faɗimatu ɗiyar Annabi, babu wasu Jikokin Annabi (Hassan da Hussaini), yazo sai a tabbatar masa da samuwar su a tarihi da tarin falalar su.
7. Yace: Shi ɗan Kur'ani zalla ne, a tambaye shi a ina ya samo Alkur'anin da yake tutiya dashi? Wahayi aka yi masa? Ko a mafarki aka ba shi?
8. A tambaye shi menene fa'idar aiko da Alkur'ani ta hannun Annabi, idan ba domin ya bayyana ma mutane abin da aka saukar masu ba ne.
9. Menene abin da yau za mu gani da zai nuna gadon aikin fassara/ƙarin bayani da Manzon Allah (SAW) ya yi akan AlKur'anin da aka saukar masa?
10. Akwai wasu surori da ayoyi da muke so a tambaye shi inda ya samo fassararsu tunda bai yarda da fassarar da aka ruwaito daga Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ba.
In har ya bada amsa dai-dai, sai ya koma gida cikin uzza, amma ina ya kasa kuwa yana da zaɓi kamar haka
1. Ya tuba daga waɗannan ƙazantattun maganganun sa. Ya koma makaranta domin a koyar dashi haƙiƙanin addinin Musulunci.
2. Ya fito ƙarara ya bayyana addinin da yake bi daban da wanda Annabi (SAW) ya zo dashi.
Kuma mun sani a dokokin Najeriya, yana da ƴancin ya yi duk abin da ya so ya yi, in ya ga dama yace: Kur'anin ma bai yarda da wani kaso ba, amma dai ba Musuluncin da Annabi Muhammad (SAW) ya zo da shi.
Allah ya muke roƙo daya bayyanar da gaskiya, ya taimaki masu gaskiya, ya ba mu ikon bin ta, ya rusa ƙarya da ma'abotanta.
Ibrahim Musa,
Safiyar Juma'a 30/5/1447 (21/11/2025).
