Isra’il ta ci gaba da kai munanan hare-haren bama-bamai a Zirin Gaza, inda ta sake luguden wuta a wurare da dama yayin da yakin ke ƙara tsananta.
A gefe guda kuma, dakarun Isra’ila sun harbe sun kashe mutane biyu ‘yan Falasɗinu a Gabashin Urushalima da aka mamaye, a cewar rahotannin yankin da hukumomin lafiya na Falasɗinu. Shaidu sun ce an yi musayar gardama a yankin kafin dakarun Isra’ila su bude wuta.
Ci gaba da hare-haren a Gaza ya kara jugunta wa yankin, tare da ƙara tsananta matsalar jin kai yayin da asibitoci ke fama da ƙarancin man wutar lantarki, magunguna da sauran kayan aiki.
Kasashe da dama na ci gaba da kira da a dakatar da yaki, amma har yanzu babu wani sabon ci gaba a tattaunawar diflomasiyya.