A ranar ƙarshe ta taron sauyin yanayi na COP30, rikici ya ƙara kamari yayin da ƙasashen duniya suka kasa samun matsaya ɗaya kan batun rage amfani da man fetur.
Wasu kasashe, musamman wadanda ke fama da matsanancin tasirin sauyin yanayi, sun matsa lamba a yi alkawarin daina amfani da makamashin fossil gaba ɗaya, suna gargadin cewa duniya na dab da ketare iyakar dumamar yanayi.
Sai dai kasashen da ke da arzikin man fetur da gas sun yi watsi da wannan kira, suna nanata cewa makamashin fossil ba zai gushe daga tsarin samar da makamashi ba nan da shekaru masu zuwa, suna mai cewa fasahar kama hayaki (carbon capture) ita ce ya kamata a mayar da hankali a kanta, ba daina amfani da man ba.
Masu tattaunawa sun yi aiki har cikin dare domin cimma matsaya, amma har aka rufe taron ba a samu cikakkiyar yarjejeniya kan batun man fetur, kwal da gas ba. Masana sun ce wannan rarrabuwa na nuna yadda siyasar makamashi ta ƙara rikitar da kokarin kare muhalli duk da yadda tasirin dumamar yanayi ke ta’azzara.
An rufe taron da ɗan cigaba a wasu ɓangarori, amma manyan batutuwa kan man fetur sun rage a buɗe, abin da ke nufin tattaunawa za ta ci gaba a sauran tarukan duniya masu zuwa.