Gwamnatin jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin gwamna Malam Umaru Dikko Raɗɗa ya bayar da umarnin kulle makarantun Firamare da Sakandire har sai Mama ta gani.
Ma'aikatar makarantun Firamare da Sakandire ƙarƙashin jagorancin kwamishina Hon. Yusuf Sulaiman Jibia, ya bayar da umarnin rufe dukkan makarantun ne a yau Juma'a 21/11/2025, har sai Mama ta gani. An ɗauki wannan matakin ne saboda matsalar tsaro da ta addabi jihar da maƙwabtanta.
Idan ba ku manta ba, a kwanakin baya, gwamnatin jihar, ta kafa kwamiti domin bibiyar sulhun da da yawa daga cikin ƙananan hukumomin jihar suka yi da 'yan ta'addan daji.
Kwatsam kuma a satin da ya gabata ne, aka samu wasu 'yan ta'adda suka shiga makarantar kwana da ke jihar Kebbi suka yi awon gaba da ɗalibai mata har guda 25 tare da kashe mutum guda daga cikin malamansu.