Yan Ta'adda Sun Sake Fasa Wata Makaranta Sun Kwashi Dalibai

Gwamnatin Neja ta ɗora alhakin sace ɗaliban makarantar St. Mary's Catholic School da ke Papiri, ƙaramar hukumar Agwara, kan ƙin biyayya ga umarnin tsaro da aka bayar tun da farko.
A wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin jihar, Abubakar Usman ya fitar, gwamnati ta ce: "Lamarin abin takaici ne, wanda za a iya daƙle shi, idan da an yi biyayya ga rahoton tsaro da aka samu tun farko.” Domin bayanan sirri sun riga sun nuna yiwuwar kai hari a yankin na Neja ta Arewa.
Gwamnati ta bayyana cewa ta ba da umarnin rufe makarantun a yankin, amma St. Mary’s ta yi shagulatun ɓangaro tare da buɗe makarantar ba tare da neman izini ko sanar da hukuma ba.
Har yanzu, hukumomin tsaro na ci gaba da tantance adadin ɗaliban da aka sace a makarantar, a harin da aka kai tsakanin ƙarfe biyu zuwa uku na safiyar ranar Juma’a 22/11/2025.
Har ila yau, an kuma fara aikin ceto, gwamnatin Neja ta tabbatar wa al'umma cewa tana aiki tare da jami’an tsaro domin ganin an kuɓutar da dukkan waɗanda aka sace.
Gwamnatin ta yi kira ga makarantu da shuwagabannin al’umma da su bi shawarwarin jami'an tsaro, tana mai cewa tsaron ɗalibai shi ne babban fifiko gare ta.

Post a Comment

Previous Post Next Post