Rahotanni daga Dubai sun tabbatar da cewa jirgin yaƙi na India mai suna Tejas ya fado yayin gudanar da Dubai Airshow, lamarin da ya yi sanadin rasuwar matuƙin jirgin.
Shaidu sun ce jirgin ya fara rawar jiki ne a sararin sama jim kaɗan bayan fara nuna bajintarsa, kafin daga baya ya faɗo ƙasa ya kama da wuta.
Hukumomin tsaro da na gaggawa sun isa wurin cikin lokaci, amma matukin bai tsira ba sakamakon mummunan fashewar da ta biyo bayan fadowar.
India ta ce za ta fara cikakken bincike domin gano musabbabin hatsarin, musamman ganin cewa Tejas na daga cikin muhimman jiragen yaki na zamani da kasar ke alfahari da su.
Hukumar shirya taron Airshow ta bayyana cewa an dakatar da wasu daga cikin ayyukan nune-nunen jirage, yayin da ake tsaftace wurin da kuma tattara bayanai kan lamarin.