Sakataren yaƙin Amurka Pete Hegseth ya sanar da cewa ya samu ganawa da mai ba shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro Nuhu Ribadu.
Hegseth ya ce sun gana da Ribadu ne a game da batun zargin yi wa Kiristoci kisan gilla a Najeriya, inda ya ce za su ci gaba da tattaunawa domin kawo ƙarshen matsalar.Ya ce a ƙarƙashin mulkin Shugaban Amurka Donald Trump, sashen yaƙi na Amurka za ta yi aiki da Najeriya domin kawo ƙarshen kisan gilla da ya ce mayaƙa masu iƙirarin jihadi suke yi wa kiristoci.