Ba A Sace Dalibai A Nasarawa Ba - Ƴansanda

Rundunar ƴansandan jihar Nasarawa ta ƙaryata rahotannin da ake yaɗawa cewa an sace wasu ɗalibai biyu a makarantar St. Peter’s Academy da ke yankin Rukubi na jihar.

A wata sanarwa da kakakin rundunar ya fitar a ranar Juma'a, kakakin rundunar Ramhan Nansel wanda ya yi magana a madadin kwamishinan ƴansandan jihar Shetima Mohammed, ya ce labarin ƙanzon kurege na.

Sanarwar ta ce duk labaran da ake yaɗawa cewa mahara sun kutsa makarantar da ke ƙaramar hukumar Doma, "shaci-faɗi ne kawai aka ƙirƙira."

"Abin da ya faru shi ne wasu ɗaliban makarantar ne suka hango mafarauta suna wucewa ɗauke da bindigar farauta, sai suka ji tsoro suka saboda suna tunanin ƴanbindiga ne sai suka tsere," in ji shi kamar yadda tashar Channels ta ruwaito.

Post a Comment

Previous Post Next Post