Helen, 'yar Kasar Amurka ce, tana da mabiya samada miliyan 3 a Instagram, kuma shahararrun mawaƙa irin su Rihanna da Miley Cyrus su na bin ta a shafinta na Instagram.
Helen Ruth Elam Van Winkle, wanda aka fi sani da Baddie Winkle, ta kasance shahararriyar 'yar Intanet a Amurka, wacce ta zama abin burgewa a duniya a cikin shekarunta 80, saboda jajircewarta na rayuwar kuruciya. Ta rasu a ranar 4 ga Satumba, 2025, tana da shekara 97.
Ta fara shahara ne a cikin 2014, tana da shekaru 85, lokacin da jikarta, Kennedy, ta saka hotonta sanye da gajeren wando da yankakkiyar riga a Instagram. Hoton da sauri ya zagaya yanar gizo.
Manyan kamfanoni irin su Missguided, Smirnoff, Urban Decay, da Aussie hair care, sun ba ta hajarsu domin tallatawa. An buga littafi rayuwarta, Baddiewinkle's Guide to Life, a cikin 2017.
