Yaƙin Koriya (25 ga Yuni 1950 - 27 ga Yuli 1953) wani rikici ne na makamai a yankin Koriya da aka yi yaƙi tsakanin Koriya ta Arewa (Jamhuriyar Dimokaradiyya ta Koriya; DPRK) da Koriya ta Kudu (Jamhuriyar Koriya; ROK) da ƙawancensu. Koriya ta Arewa tana samun goyon bayan Jamhuriyar Jama'ar Sin da Tarayyar Soviet, yayin da Koriya ta Kudu ke samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya (UNC) karkashin jagorancin Amurka. Yaƙin ya ƙare a cikin 1953 ba tare da sanya hannu kan wata yarjejeniya ba.
Yaƙin Koriya ya kasance daga 1950 zuwa 1953, a lokacin da Koriya ta Arewa mai ra'ayin gurguzu (da ke samun goyon bayan China da Tarayyar Soviet) suka yi yaƙi da Koriya ta Kudu mai adawa da kwaminisanci (da Amurka ta goyi baya).
Yakin ya fara ne lokacin da sojojin Koriya ta Arewa suka tsallaka layi na 38, layin da ya rarraba tsakanin Koriya ta Arewa da Koriya ta Kudu wanda aka tsara bayan da aka yi galaba a kan 'yan mamaya na kasar Japan a yakin duniya na biyu.
A karkashin Shugaban Amurka Henry Truman, Amurka ta shiga yakin don kare Koriya ta Kudu bisa ka'idar Truman. Majalisar Dinkin Duniya ma ta ba da tallafi, amma Amurka ta ba da kashi 90% na sojoji. Bayan nasarar da Koriya ta Arewa ta yi da farko, sojojin Amurka sun tura Koriya ta Arewa baya. A Lokacin da sojojin Amurka suka tsallaka suka shiga Koriya ta Arewa. China ta aika da agajin sojojinta zuwa Koriya ta Arewan.
Daga nan ne aka kori sojojin Amurka da Koriya ta Kudu kafin daga baya su sake samun nasara. A da Shugaba Truman bai so ya shiga cikin yakin ba, yana tsoron farkewar yakin basasa, kuma ya fara tattaunawar zaman lafiya da Koriya ta Arewa a watan Yulin 1951.
Tattaunawar zaman lafiya da aka kammala a cikin yarjejeniyar da aka rattabawa hannu a watan Yulin 1953, wanda ya dakatar da yakin, ya karfafa rarrabuwar kawuna na Koriyoyi guda biyu a layi na 38 daya rabasu, kuma ya samar da yankin da ya kai tsawon kilomita 4,000.
Kusan mutane miliyan biyar ne suka mutu a yakin, yayin da fararen hula sama da miliyan 2.7 suka jikkata, yayin da sama da Amurkawa 30,000 suka mutu.
