Kamar sauran ƙasashen duniya, Falasdinu ita ma tana da tata tuta, kuma kowane launi ko zane a jikin tutar yana da tasa ma'ana. Ga yadda ma'anar take:
Launin ja: Yana wakiltar shahidai da dama da sadaukarwar al'ummar Palasdinu.
Launin Baƙi: na wakiltar zalunci da tauye hakkin Falasdinawa da suka sha na tsawon shekaru marasa adadi.
Launin Fari: alamar aminci da soyayya, da tsarkin saƙon da aka aiko kowane Annabi da su zuwa ƙasar Falasdinu mai alfarma.
Launin Kore: yana nufin wadata, albarka, da bege ga kyakkyawar makoma.
