Yakin Rasha da Ukraine: Jami’an Amurka da Turai Za Su Tattauna Kan Sabon Shirin Trump

 Ana ci gaba da rikici a gabashin Turai, yayin da rahotanni suka nuna cewa manyan jami’an Amurka da Turai za su gudanar da wata muhimmiyar tattaunawa kan sabon shirin da shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar dangane da tsagaita wuta a Ukraine.

Bisa bayanai daga majiyoyi, tattaunawar za ta mayar da hankali kan yadda shirin zai shafi dangantaka tsakanin ƙasashen yammacin duniya da Ukraine, da kuma tasirin da zai iya yi kan yadda ake tunkarar Rasha a yakin da ya ɗauki tsawon lokaci.

Masu sharhi na siyasa suna cewa wannan tattaunawar na iya zama mataki na farko na sabbin manufofi, musamman idan aka yi la’akari da tasirin da shirin Trump zai iya yi kan tsaron Turai da makomar yaki.

A halin yanzu, luguden wuta tsakanin Rasha da Ukraine na ci gaba a sassa daban-daban, yayin da kasashen duniya ke bibiyar yadda wannan sabon yunƙuri zai kare.

Post a Comment

Previous Post Next Post