Gwamnatin Jihar Neja ta sanar da rufe duk makarantun jihar saboda dalilai na tsaro, kamar yadda rahoto ya nunar.
A cikin wata sanarwa da ma’aikatar ilimi ta jihar ta fitar, an ce matakin ya zama dole domin tsare rayukan dalibai da ma’aikatan makarantu, musamman a wasu yankunan da ake fama da tashin hankali.
Gwamnatin ta ce za ta bi diddigin dukkan rahotannin barazanar tsaro, tare da tabbatar da cewa an dawo da zaman lafiya kafin makarantun su sake bude.