Kotun ƙungiyar Houthi da ke birnin Sanaa ta yanke wa mutum 17 hukuncin kisa, bisa zargin cewa suna yin leƙen asiri da aika bayanan sirri ga Isra’ila da wasu ƙasashen Yammacin duniya.
Rahotanni daga yankin sun nuna cewa waɗanda ake zargin an gurfanar da su a gaban kotu ƙarƙashin dokokin da Houthi ke amfani da su tun bayan da suka mamaye Sanaa, inda aka ce sun aikata manyan laifuka na cin amanar ƙasa.
A cewar hukumar shari’ar Houthi, waɗanda aka yanke wa hukuncin kisan sun yi amfani da na’urorin sadarwa da hanyoyin intanet wajen aika bayanai da bayanan sirri ga hukumomin kasashen waje, duk da cewa ba a bayyana ƙarin cikakkun bayanai kan hujjojin da aka gabatar ba.
Har yanzu ba a ji ta bakin iyalan waɗanda aka yankewa hukuncin ko lauyoyinsu ba, yayin da ƙungiyoyin kare haƙƙin bil’adama suka bayyana damuwarsu cewa shari’ar ba ta bi ka’idojin shari’a ta gaskiya ba, musamman ma a yanayin rikicin Yemen da ya daɗe yana cigaba.
Kungiyar Houthi dai ta sha tuhumar mutanen da suka kama da zargin leken asiri ko aiki da Isra’ila ko Amurka, musamman a wannan lokacin da ake ƙara samun tashin hankali a yankin Gabas ta Tsakiya.
Har yanzu hukumomin ƙasashen da aka ambata ba su fitar da wani martani kai tsaye ba kan wannan hukunci.